Mata Da 'Yan Mata Aka Fi Safarar Su Zuwa Kasashen Larabawa Ko Turai-MDD

Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Dr. Amina Mohammed

Wani rahoton hukumar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai kula da kaurar jama’a wato IOM ya gano cewa galibin mutanen da ke shiga hannun masu safarar mutane akan hanyoyin dake ratsa Jamhuriyar Nijer zuwa kasashen Larabawa da na yammacin duniya mata ne da ‘yan mata suke shiga tashin hankali.

Kimanin mutane 666 daga cikin wadanda suka fada tarkon masu safarar bil adama ne aka ajiye a cibiyar OIM mai kula da ‘yan cirani dake Zinder daga shekarar 2017 zuwa 2021 a cewar rahoton hukumar ta IOM wanne ya kara da cewa kashi 69 daga cikinsu mata ne da ‘yan mata.

Wadanan mutane an yi masu rajista ne a Zinder da Agadez da Arlit da Dirkou da birnin Yamai abin da ke nunin yadda fataucin mutane ke neman zama ruwan dare a wannan kasa duk da matakan da mahukunta ke dauka. Daliba a wata makarantar ilimin kimiyar na’ura mai kwakwalwa Shamsiya Sabo na mai alakanta wannan al’amari da wasu tarin dalilai.

Rahoton ya ambato wakiliyar hukumar OIM a Nijer Barbara Rijks ta na cewa kyakkyawar fahimtar da ake samu a ayyukan hadin guiwar dake tsakaninsu da hukumomin kasar ta taimaka sosai wajen gudanar da wannan bincike da zai bada damar tallafawa wadanan mutane. Shugabar kungiyar kare hakkin mata ta APAISE Hadjia Rabi Djibo Magaji na da irin wannan ra’ayi.

Haka kuma ana gano cewa kashi 56 daga cikin 100 na wadanan mutane ‘yan Najeriya ne dake neman ratsa Nijer don zuwa kasashen yammaci yayinda kashi 23 daga cikinsu ‘yan Nijer ne sannan sauran kan fitowa ne daga kasashen yankin kudu da sahara.

Dan rajin kare hakkin jama’a Dambaji Son Allah mamba ne a kwamitin hadin guiwar hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu CNLTP mai yaki da fataucin mutane.

Kashi 38 daga cikin 100 na wadanda da aka ajiye a cibiyoyin kula da bakin haure mutane ne da aka saka cikin harakar kasruwanci kokuma ake kokarin shigar da su cikin wannan haraka yayin da kashi 21 daga cikinsu ana ci da guminsu ta hanyar aikatau da wasu sauran ayyukan karfi sai kashi 23 na rukunin wadanda aka tilastawa shiga sana’ar bara a cewar hukumar OIM.

Souley Moumouni Barma ya aiko mana wannan rahoto daga birnin yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Da 'Yan Mata Ne Aka Fi Safarar Su Zuwa Kasashen Larabawa Ko Turai-MDD