Mata da Matasa Zasu Kai Labari Kuwa?

Matasa Maza da Mata

A yanzu haka ana jiran sakamakon zaben gwamna da 'yan majalisun jiha a ga matasa da mata nawa ne za su kai labari.

Matasa da mata a siyasar Najeriya ba su faye samun nasarar tsayawa takara ba sai dai rike 'yan mukamai bayan gwagwarmayar kamfe da a wani lokacin matasan maza kan auka bangar siyasa.

Wannan karon matasa sun tsaya takara kama daga kan neman gwamna,yan majalisar wakilai da dattawa.

Binta Garba ita ta lashe zaben majalisar dattawa daga Adamawa ta arewa da yin nasara kan gwamna Bala Ngillari, ta ce takaicin kuncin da jama'a ke ciki ne ya ba ta kwarin guiwa har ta samu shiga siyasa.

Manyan jam'iyyun Najeriya PDP da APC sun tsaida 'yan takarar gwamna tsaran juna a jihohi da dama kamar Neja,Kaduna da Adamawa inda Taraba ke da mace daya tilo da ke takarar gwamna da ke samun mara bayan shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari.

Ga matashi Bindo Jibrilla ga Nuhu Ribadu na kalubalantar juna a Adamawa. wannan siyasa nada dinbin tarihi a Najeriya.

A yanzu haka ana jiran sakamakon zaben gwamna da 'yan majalisun jiha a ga matasa da mata nawa ne za su kai labari.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Mata Da Matasa Zasu Kai Labari Kuwa? - 1'30"