Kakakin gwamnatin jihar Kano Mallam Jafar-Jafar yayi kira ne da masu jefa kuria da suyi hattara da zaben tumun dare a zaben gwamnoni.
‘’Idan ka zabi shugaba can sama aikin sa daban idan ka duba zaka ga cewa ayyukan gwamnatin tarayya aikin ta ba yawa ne suke dashi ba, wanda gwamnatin jihar tayi yawanci su suka fi yawa, gwamnatin jiha ita ce mafi kusanci da jamaa bayan karamnmar hukuma, kuma asusun karamar hukuma a hannun gwamnatin jiha yake akwai abinda ake cewa JOINT ACCOUNT asusun da ake hada kudaden waje daya hukuma bata isa ta kashe wasu kudi ba sai gwamnatin jiha ta bata umurni ta kashe wadannan kudade zata yi wa jamaa aiki dashi idan har taga cewa bai kamata a kashe wadannan kudaden ba to kaga ba a kashe su ba.
Sabo da haka yakamata jamaa atsaya a duba wannan zaben mai matukar mmuhimmamci ne kamar yadda akayi zaben shugaban kasa akayi aka gama lafiya, wannan zaben ma yakamata ace an zo an zabi wadanda aka ga sun dace, mutane su tsaya su duba cancanta, su duba jajircewa su duba makamar aiki su zabi wanda suka ga ya dace su zaba, sabo da haka bai kamata mutane su dauki raayin zuciyar su ba yakamata ka dub aka gani cikin ya takarkarin wanene mai jajircewa, kar kaje ka zabi magen lami wadda ba yakushi ba cizo kuma bata kama bera.
Gwamna mutum ne mai jajircewa mai sanin makamar aiki ba wanda idan ya dauki kudin jamaa ya dauke kansa ba ko kuma ayi ta wadaka da kudin al’umma yakamata jamaa su tabbatar sun duba wadannan halayyar da yan takarkarin da zasu zaba, yan majilisun jiha suma da za a zaba, wato yakamata jamaa su tsaya su lura cewa shima zabe nee mai muhimmamci domin yan majilisun jiha su suke yin dokokin da ake tafiyar da gwamnatin jiha, idan gwamnatin jiha tayi ba dai-dai zasu karkata akalar ta su kai ta inda yafi cancanta.
Idan har aiki ne ne gwwamnatin jiha keyi to majilisar jiha it ace ke dubawa akwai abinda ake kira da turanci cewa Over Sight Function zata je ta duba shin wannan abinda gwamnati take yi haka ne ko kuma ya dace ayi shi, idan bai dace ba sai ta lurar da gwamnatin jiha tace mata a’a wannan abu bai dace ba, yakamata ace jama sun duba sun gani a matakin majilisu su duba su zabi shugabanni na gari, shugabanni nagari sune zau tabbatar da ci gaban al’umma shi yasa kasashen da suka ci gaba zaka ga kananan hukumomin su suna da yawa domin idan babu hukuma kusa da jamaa zaka ga abu ya baci kafin a gyara shi sai ayi wata da watanni yanzu ko rami ne a bakin hanya idan ace gwamnati a matakin gwamnatin tarayya zata gyara kafin azo a gyara shi sai ayi shekara ba a zo ba amma da yake akwai matakin jiha jamiaan ta suna kusa da jamaa sunga wannan matsalar sunkai koke nan danan sai kaga anzo an gyara shi.
Don haka wannan zaben kamar wancan da akayi sati biyu da suka wuce to wannan ma jamaa su jajirce su fito su zabi wadanda suka dace a zaba.