Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfe Na Bayan Fage Zai Yi Tasiri Kuwa?


Rige-rigen shawo kan al’umma don zaben gwamnoni a shiyar arewa maso gabas a tsakanin manyan jamiyyu biyu wato APC da PDP naci gaba a bayan fage bayan rufe kamfe din da aka yi ukku daga cikin gwamnoni shidda dake yankin suna neman ta zarce ne, da suka hada da Ibrahim Gaidam,na Yobe Kashim Shattima na Borno, da Ibrahim Hassan Dan kwambo na Gombe,Isah Yuguda ma fatan ganin Awal Jatau ya gaje shi, a bayan dashi Yugudan yasha kaye a zaben Sanata.

Sanin kowa ne matasa masu tada kayan baya sun haddasa mutuwar mutane da kuma dukiyoyi masu dinbin yawa a shekara ta dubu biyu da goma shadaya da sunan masu mara baya ga yan takara.

Masanin siyasa Kolo Shatimma yace ba za a samu rigingimu a wannan zaben ba kamar ta dubu biyu da goma sha daya ba.

‘’Koda yake ba agama zaben gaba daya ba a fadi sakamako da sauran su idan za mu iya tunawa wajen mutane 927 aka kashe a zaben 2011’’

Sai dai yawan canjin sheka daga PDP zuwa APC na nuni da cewa akwai lauje cikin nadi, amma cewa mataimakin kakaki jamiyyar PDP na kasa Barister Abdullahi Jalo masu irin wannan hali suna da kasha ne a gindi su.

‘’Mutane dake canza sheka a harkar siyasa kullun ka tsaya akan raayin ka jamiyyar idan ta tashi neman mutane ta neme ka da mutuncin ka amma yayin da ka kai kanka, ka zamo dan siyasan dake jiran asa wa burodi bulu band yaci abu ne yake so da sauki mutane sunyi aiki shi yazo ya dauki kason da mutane suka sha wahala akai, ya maida mutane basu da wayo wannan shine kawai zan fada mutane da suke irin wannan a wannan lokaci’’

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG