A yayin da ake ta kokarin tantancewa da kada kuri’u a fadin Najeriya, mata da matasa na taka rawar gani musamman yadda ake fafatawa da da mata da matasa sabbin jini wajan takarar kujeru daban daban.
Hajiya A’isha Jummai Alhasan itace mace kadai ‘yar takarar gwamna a jahar Taraba kuma a hirarmu da ita, tayi bayanin cewa daya daga cikin dalilan da yasa ta shiga wannan takara a matsayinta na mace shine irin danniya da da tsoro da ake alakanta su dashi bai kamata ba.
Ta kara da cewa duik abin da maza kanyi mata ma wakazalika, kuma wannan wata dam ace ta nuna wa sauran mata cewar lallai suma ya kamata su mike domin a rika damawa da su a demokaradiyyar kasar.
Ta fannin matasa kuma, da dama sun kasance cikin takarar kujeru daban daban kamar dantakara gwamnan jahar Naija da Kaduna dama sauran wasu kujeru daga jahohi zuwa kananan hukumomi.
Najeriya ta fara samun wannan dama ta matasa masu kananan shekaru da mata a fagen siyasa wanda hakan zai taimaka wajan ciyar da kasar gaba, da kuma kara yiyuwar dorewar sahihiyar demokaradiyya da zaman lafiya a kasar.