Masu Zanga-Zanga Sun Taru A Legas Da Abuja Kan Tsadar Rayuwa

  • VOA Hausa
A ra'ayoyinsu, ba a bukatar shagulgula a wannan likaci amma sun bukaci gwamnatin Shugaba Tinubu ta shawo kan matsalolin hauhawar farashi da tsadar rayuwar da ba'a taba ganin irinta ba a tarihin kasar.

A yayin da Najeriya ke bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallakar Burtaniya a yau Talata, dubban al'ummar kasar ne suka taru a manyan cibiyoyin siyasa da tattalin arzikin kasar;biranen Abuja da Legas domin nuna adawa da tsadar rayuwa da makamashi a kasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka.

A ra'ayoyinsu, ba a bukatar shagulgula a wannan likaci amma sun bukaci gwamnatin Shugaba Tinubu ta shawo kan matsalolin hauhawar farashi da tsadar rayuwar da ba'a taba ganin irinta ba a tarihin kasar.

An yayata batun zanga-zangar ta ranar 1 ga watan Oktoban bana mai taken "fearlessinoctober" a kafafen sada zumunta, watanni 2 bayan wacce ta gudana a watan Agustan daya gabata mai taken "endbadgovernance". Dukkanin zanga-zangar 2 sun yi kama da juna akan manufa inda fusatattun matasa suka bukaci a dawo da biyan tallafin man fetur tare da janye karin kudin lantarki.

A yau Talata, masu zanga-zangar sun taru a yankin Utako na Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya suna daga tutar kasar mai launin kore da fari da kore da kwalaye masu sakonni irinsu "a kawo karshen rashin iya mulki" da (a kyale 'yan najeriya mazauna ketare su yi zabe" da kuma "a kawo karshen tsadar rayuwa ".

A Legas, haka al'amarin ya kasance a kewayen babban birnin jihar Ikeja, inda matasa suka mamaye shahararren yankin gadar kasan Ikeja, inda suka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a ranar da gwamnati ta ayyana hutu domin shagulgulan bikin 'yancin kan Najeriya.