Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tawartsa Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Abuja, Legas


Masu zanga-zanga a Legas
Masu zanga-zanga a Legas

Masu zanga-zangar sun taru a yankin Utako na Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, suna daga tutar kasar da kwalaye masu dauke da sakonni irinsu "a kawo karshen rashin iya mulki" da "a kyale 'yan Najeriya mazauna ketare su rika zabe" da "a kawo karshen tsadar rayuwa" .

A yau Talata, jami'an 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye akan masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta "fearless in October", a biranen Abuja da Legas.

Masu zanga-zangar sun taru a yankin Utako na Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, suna daga tutar kasar da kwalaye masu dauke da sakonni irinsu "a kawo karshen rashin iya mulki" da "a kyale 'yan Najeriya mazauna ketare su rika zabe" da "a kawo karshen tsadar rayuwa" sai dai 'yan sanda sun tarwatsa su.

An yayata batun zanga-zangar ranar 1 ga watan Oktoba ta bana mai taken "fearlessinoctober" watanni 2 bayan wacce ta gudana a watan Agusta mai taken "endbadgovernance"a kafafen sada zumunta.

Dukkanin zanga-zangar 2 sun yi kama a manufa kasancewar fusatattun matasa ke fafutukar ganin an dawo da tallafin man fetur tare da janye karin kudin lantarki.

Farashin makamashi ya ninka fiye da sau 3 tun bayan da Tinubu ya karbi ragamar mulkin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Farashin litar man fetur ta tashi daga Naira 200 zuwa fiye da dubu 1 yayin da kudin lantarki ya rubanya sau 4, inda ya yi mummunan tasiri akan bangaren masana'antu da kuma tattalin arzikin 'yan Najeriya.

A jawabinsa yayin bikin murnar zagayowar ranar 'yancin kan Najeriya karo na 64 a yau Talata, Tinubu ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri tare da bashi karin lokaci, inda yace gwamnatinsa na sake nazarin manufofin tattalin arzikinta domin kyautata rayuwar 'yan Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG