Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Takaita Bikin Samun ‘Yancin Kai – Gwamnatin Borno

Gwamna Zulum na jihar Borno (Facebook/Gwamnatin Borno)
Gwamna Zulum na jihar Borno (Facebook/Gwamnatin Borno)

Kwamishinan Watsa Labarai da Tsaron Cikin Gida na jihar, Farfesa Usman Tar, ya sanar da wannan shawarar rage bukukuwan ne a wata sanarwa a ranar Litinin.

Gwamnatin Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce za ta takaita bukukuwan bikin samun ‘yancin kai a wannan shekara.

A farkon watan Satumba ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan birnin Maiduguri lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, wannan ambaliyar ruwa ita ce mafi muni da birnin ya ganin cikin shekaru 30

Kwamishinan Watsa Labarai da Tsaron Cikin Gida na jihar, Farfesa Usman Tar, ya sanar da wannan shawarar rage bukukuwan ne a wata sanarwa a ranar Litinin.

Ambaliyar ta yi barna mai tsanani da ta shafi daruruwan iyalai tare da lalata muhimman ababen more rayuwa kamar asibitoci, makarantu, hanyoyi da gadoji.

"Gwamnati za ta karkatar da kudaden zuwa ga gyaran ababen more rayuwa da ambaliyar ta lalata, kuma za ta samar da tallafi ga mutanenmu.” Wani bangare na sanarwar ta Tar ta ce.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG