Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bukaci jam’iyyar APC mai mulki da ta sauya akalar abin da ta kira “tsare-tsaren da suke kuntatawa” al’umar kasar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar jajiberin bikin ranar samun ‘yancin kasa, dauke da sa hannun kakakinta, Debo Ologunagba, PDP ta ce APC ta yi wa ‘yan Najeriya alkawura da dama wadanda ba ta cika ba.
Daga cikin kiran da jam’iyyar adawar ta yi har da batun rage kudin man fetur da aka kara a farkon watan Satumba.
“Ya kamata ba tare da bata lokaci ba, Gwamnatin Tarayya ta rage farashin man fetur da kuma dakile faduwar darajar Naira ta hanyar sake tsara albarkatu domin farfado da sashen samar da kayayyaki da ke tangal-tangal.” Sanarwar ta ce.
“Akwai bukatar APC ta fahimci cewa Najeriya kasa ce mai 'yancin kai kuma mulki yana hannun mutane.”
“Saboda haka, ya zama dole gwamnati karkashin jagorancin APC ta saurari 'yan Najeriya ta sake duba dukkan manufofi da ayyukan da ba sa amfanar da jama'a wadanda ke takura rayuwa a kasar.” Sanarwar ta ce.
Sanarwar ta kara da cewa, “hakika, 'yan Najeriya suna cikin radadi! Dole ne ya dauki mataki yanzu ta hanyar karkatar da albarkatu zuwa ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga jin dadin 'yan Najeriya.”
A baya, shugaban kasa Bola Tinubu ya sha bayyana dalilan da suka sa aka cire tallafin mai yana mai cewa gwamnati na barnar kudi.
A cewar Tinubu ‘yan Najeriya sun fi amfana da cire tallafin mai duk da cewa rahotanni na nuni da akasin hakan duba da yadda kayayyaki suka tashi.
Dangane da karin kudin mai da aka yi a kwanakin baya, Tinubi ya ce wannan hurumi ne na kamfanin mai na NNPCL, wanda ya ce ana bin sa daloln biliyoyi a matsayin bashi.
Sanarwar ta PDP na zuwa ne a ranar jejeiberin samun ‘yancin kasa yayin da Najeriya ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Dandalin Mu Tattauna