Masu Tada Kayar Baya Sun Fusata Da Gwamnatin Trump

Masu Zanga Zanga a Amurka

Masu zanga zanga a Amurka sun bayyana fushi da damuwarsu ga gwamnatin Trump, a kan shirinta na raba ‘ya'yan bakin haure da iyayensu.

Daruruwar masu zanga zanga sun yi cincirundo a harabar ofishin ma'aikatar shige da fice a SanFrancisco, a jiya Talata, suna ihu suna cewa a hada iyalai wuri daya.

Daya daga cikin masu zanga zangar ta bayyana matukar fushinta a kan shugaba Donald Trump, tana rungume da tutar Amurka tana jawabi a kan bakin haure a jiya Talatan.

Tace shin wanenen ya san halin da wadannan kananan yaran ke ciki? Shin wanene zai iya gane damuwarsu? Tace dazu naga Trump rungume da tuta. Shin amsar shi kenan? Ya rungume tuta? Alhali kuwa wadannan bakin hauren basu iya rungumar ‘ya'yansu. Wannan mugun hali ne. Akwai miyagu kuma bana kaunarsu.

A nan Washington, Trump ya gamu da fushin wadansu 'yan Democrat yayin da ya isa majalisar majalisar dokokin kasar a jiya Talata domin ya gana da wakilan ‘yan Republican a kan neman hanyar warware wannan batu dake neman zama babbar kalubala.

Yace mun samu tattaunawa mai amfani. Wadannan dokoki ne da aka karyasu shekaru da dama, amma dai mun yi tattaunawa mai amfani.