Masu Sharan Asibiti Suke Sawa Mutane Jini

Kasar Kamaru ta maido da wasu ‘yan gudun hijira wadanda zuwa Najeriya, kamar yadda bayanai ke nunawa kasar ta Kamaru tana maido da sune saboda an yi mata yawa,.

Su kansu ‘yan kudun hijiran sun kagarasu komo gida ganin cewa lamura sun fara daidaita.

Hukumomin tsaro tare da jami’an bada agaji ne suka tarbi ‘yan gudun hijiran dake komowa a bakin iyakar Najeriya, da Kamaru, kuma akasarinsu sun fito ne daga garuruwa Bam,a, Baki da kuma Gamburu Ngala dake jihar Borno.

Jami’in hukumar NEMA, mai kula da sansanoni ‘yan kudun hijira dake Yola, Alhaji Sa’adu Bello, ya shaidawa wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdulazeez, cewa akasarin mutane suna cikin koshin lafiya.

Sai dai yayi da jami’an, hukumar da NEMA, ke karbar mutanen da aka maido daga Kamaru, ta iyakar Mubi, su kuwa shuwagabanin al’umomin yankin na kokawa game da matsalar rashin Likitoci a babban Asibitin garin Mubi, wanda ke kula da kanana hukumomi biyar.

Dan majalisar jihar Adamawa mai wakiltar mazabar Mubi, ta kudu Abubakar Abdulrahaman, yace “Likita daya ne ke kula da jama’a, a asibitin dake kula da kanana hukumomi biyar ace Likita daya shine zai yi aiki awowi ashirin da hudu kaga akwai abun damuwa, baya da muka je muka ga asibitin sai Likitan ke gayamana cewar watarana ma masu sharan Asibiti suke sama mutane jini, idan ya kare suke cirewa.’