Kungiyoyin fararen hula da na addinai na ta rusawa gwamnatin Najeriya kiran cewa lallai ta gudanar da bincike a kan kashe-kashen Apo a Abuja
WASHINGTON, DC —
Yawan wadanda aka kashe a Abuja na ci gaba da karuwa sanadiyar mutuwar wadanda ke kwance a asibiti su na jinyar raunukan da suka samu lokacin da jami'an tsaron Najeriya su ka yi mu su ruwan wuta a ranar jumma'ar da ta gabata. Wannan al'amari na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkokin fararen hula, da kungiyoyin addinai na Najeriya ke ci gaba da ziyartar sauran wadanda aka harba da ke kwance a asibiti domin su ga halin da suke ciki, kuma su yiwa hukumomin kasar Najeriya matsin lambar cewa lallai sai sun gudanar da bincike a kan wannan al'amari wanda da yawa ke gani tamkar kisan gilla ne jami'an tsaro su ka aikata. Haka kuma kungiyoyin kare hakkokin fararen hula na shirin yin zanga-zanga a Majalisar dokokin Najeriya domin tursasawa 'yan Majalisar su yi muhawara akan batun tare da bude hanyar yin bincike a kai kamar yadda ya kamata. Ga cikakken bayani a cikin rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aikowa Sashen Hausa daga birnin Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5