Abokin aiki Sahabo Imam Aliyu ya zanta da wani mutumin Kafanchan James Wuye ya san musabbabin wannan sabon tashin hankalin da ya kada al'ummar jihar. Mr. James Wuye ya bada dalilai da yawa. Daya daga cikinsu shi ne rashin aiki da shawarwarin da aka ba mahukuntar jihar. Ya ce sun kafa wani kwamiti na kawo sulhu. Sun tattauna da bangarorin biyu a duk fadin kananan hukumomin jihar kana suka bada shawara yadda za'a yi maganin irin wannan tashin tashinar a jihar Kaduna. Ya ce gwamnati ta kan bata lokaci kafin ta duba abun dake gabanta. Yin hakan sai wani abu ya taso kamar wanda ya faru a Kafanchan.
Abu na biyu shi ne rashin cika ababen da al'umma suka fitar ko kin yin anfani da shawarwari da kuma kin hukunta wadanda suka yi laifi da can.Ya ce shi yasa idan wani abu ya tashi sai mutane su tuna baya suna son daukar fansa.Ya kara da cewa wani abun bakin ciki shi ne sai a ji mutane suna kirga wadanda suka kashe a kowane bangare da wurin ibada da suka kone ko rushe kamar suna kirga kiyashi. Ya ce duk irin wadannan abubuwa talaka ne ke shan wahala.
Ga karin bayani.