Masu kada kuri’a a kasar Tunisiya zasu fita zabe yau lahadi domin zaben abinda aka kira majalisar kundin tsarin mulki da zasu rubuta wani sabon kundin tsarin mulki da kuma shata tsarin siyasar kasar dake arewacin Afrika.
Wannan ne karon farko da za a gudanar da zaben damokaradiya a kasar tunda Tunisiya ta sami ‘yancin kai a shekara ta dubu da dari tara da hamsin da shida. Sama da jam’iyu 100 suka tsaya takarar neman kujerun majalisa 217, akasin zabukan da aka gudanar a baya, inda ake tilastawa masu kada kuri’a sake zaben jam’iya mai mulki.
Da zarar an kafa sabuwar gwamnati, wakilan zasu rubuta sabon kundin tsarin mulki ya maye gurbin wanda dadadden dan mulkin kama karya na kasar Zine el-Ben ali yake amfani da shi, wanda aka hambare gwamnatinshi a juyin juya halin da aka yi a kasar cikin watan janairu. Abinda ya haifar da guguwar juyin juya halin kasashen Larabawa.
Masu kula da lamura sun yi harsashen cewa, jam’iyar ‘yan ra’ayin addinin Islama masu tsattsauran ra’ayi Ennahdha zata sami mafi yawan kuri’u sai dai ba zata sami rinjaye ba. Tuni ta fara tattaunawa da nufin kafa gwamnatin hadin guiwa