Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin kasashen duniya sun bayyana samun sauki da mutuwar Gadhafi


A surfer rides a wave on the river Eisbach in the English Garden in downtown Munich, southern Germany.
A surfer rides a wave on the river Eisbach in the English Garden in downtown Munich, southern Germany.

Shugabannin kasashen duniya suna taya mutanen kasar Libya murnar shiga wani sabon babi bayan sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar Moammar Gadhafi.

Shugabannin kasashen duniya suna taya mutanen kasar Libya murnar shiga wani sabon babi bayan sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar Moammar Gadhafi.

Sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, dake ziyarar aiki a Aghanistan ta shaidawa tashar talabijin ta FOX News cewa, tabbatar da mutuwar Gadhafi wani abu ne mai kwantar da rai. Ta kuma shaidawa tashar talabijin ta CBS cewa, duk da yake wannan yana da muhimmancin, ba lallai ne mutuwar Gadhafi ta kawo karshen fada a Libya ba.

Dan majalisar dattijan Amurka kuma tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin tutar jam’iyar Republican John McCain ya bada sanarwa yau alhamis cewa, mutuwar Gadhafi ta kawo karshen rukunin farko na juyin juya halin kasar Libya. Ya kuma yi kira ga Amurka da abokan kawancenta na kasashen turai da kuma abokan huldarsu na kasashen Larabawa su kara kaimi wajen marawa mutanen kasar Libya baya.

Babban magatardan MDD Ban ki-moon yace mutuwar Gadhafi wani tarihi ne a kafa sabuwar gwamnati a kasar Libya. Ya kuma yi kira ga mayaka su ajiye makamansu, yayinda ya yi gargadi da cewa, kasar zata iya cika alkawarinta na shata kyakkyawar makoma ta wajen hada kai da sasantawa kadai.

Kasashen turai suma sun yaba ganin bayan Gadhafi.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel sun ce mutuwar Gadhafi dama ce da kasar Libya ta samu ta komawa mulkin damokaradiya.

A nashi kalami bayan jin labarin mutuwar Gadhafi, Firai Ministan kasar Italiya Silvio Berlusconi ya bayyana cewa ‘yanzu yaki ya kare’.

XS
SM
MD
LG