Batun cinikayyar albarkatun man fetir dama yadda za a gudanar da garanbawul ga bangaren na cikin abubuwan farko da sabuwar gwamnatin Najeriya ta ayyana manufofi da tsare tsarenta.
A jawabinsa na karbar ragamar mulkin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun bana, shugaba Bola Tinubu ya sanar da matakin cire tallafin al’amarin sanya farashin man fetir a kasar ya tashi a zuwa fiye naira 500 kafin daga bisani ya koma 620.
Matakin dai ya girgiza farashin kayayyaki da aikace aikacen yau da kullum, lamarin da ya haifar da yanayin tsadar rayuwa a kasar, inda masu cinikayyar man daga yankin arewa ke cewa kasuwancinsu na cikin hadari.
Alhaji Idris Musa Garki guda cikin dattawan kungiyar IPMAN ta masu cinikayyar mai a Najeriya yace suna fuskantar kalubale. “Yanzu mu da muke safarar maid aga kudanci zuwa arewa harkar mu na neman durkushewa, saboda idan muka sayo mai akan naira 580 lita guda muna biya mata naira 40 kudin sufuri zuwa Kano, Kaduna Sokoto ko Maiduguri da sauran sassan arewacin Najeria, don haka lita daya tana zuwa mana akan naira 620 kuma ance mu sayar akan farashin naira 620 din ka ga babu riba. Amma dan kudu naira 5 zuwa 10 kacal yake biyan kudin, ya samu ribar naira 35 zuwa 30.”
Sai dai masanin tattalin arziki Dr Lawan Habib Yahya ya ce tagwayen manofofin gwamnati na musayar kudaden waje da cire tallafi sune sune dalilan tsintar kai a wannan yanayi, amma acewar sa akwai mafita.
Yana mai cewa, Kodayake Dr Lawan ya bayyana wannan tsari a matsayin na wucin gadi, amma ya ce babu laifi ace gwamnati ta sake lale gabanin ci gaba da aiwatar da shirin ta na cirewa ko janye tallafi.
“Babu laifi gwamnati ta sake bitar wannan tsari nata na janye tallafi, zata iya dawo da tallafin na wucin gadi daga bisani bayan ta kammala shirye shiryen da suka kamata sai ta cire shi, haka kashen duniya kan yi a duk lokacin da suka fito da wasu manufofi kuma aka ci karo da kalubale”
Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta ce tana sane da mawuyacin halin da ‘yan kasar ke ciki biyo bayan matakin cire tallafin da kuma tsadar musayar takardun kudin na dala.