Kungiyar tace, kowanne gwamna da ya fito da sunayen waɗanda sukaci moriyar, da kuma ababen da aka siyo domin rage zafin raɗaɗin da ƴan najeriya ke fama dashi.
Idan za'a iya tunawa Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan Biyar ga dukkanin Jihohin Ƙasar haɗi da babban birnin Abuja, domin suyi amfani dasu wajen sauƙaƙawa ƴan ƙasar bisa halin ƙunci da suka shiga biyo bayan cire tallafin man-fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi.
A sanarwar da Ƙungiyar fafutukar kare ƴancin ƴan ƙasa da kuma ƙididdigan ayyuka wato SERAP ta fitar ta hannun mataimakin Daraktan Kungiyar Kolawole Oluwadare, kungiyar tace a madadin ƴan Najeriya, tana umartar Gwamnonin Jihohi da su fito su bayyana yadda suka kashe kudin tallafin Naira Biliyan Biyu da aka basu.
A cewarsa, ƴan Najeriya na da ƴancin sanin yadda Gwamnonin suka yi amfani da kudin cire tallafin.
Ya ƙara da cewa, bayyana yadda aka salwantar da kudin ga ƴan ƙasa mataki ne na rage cin-hanci da rashawa, kuma hakan zai taimaka wajen rage wadaƙa da ta'annati.
Kolawole, ya ce za su so gwamnonin su ɗauki matakin bayyanawa ƴan ƙasar yadda suka kashe kuɗaɗen cikin kwanaki bakwai, da kuma gamsassun hujjojin da zasu tabbatar bayanansu. Idan kuma suka gaza yin hakan, to lallai su zasu ɗauki matakan da suka dace wajen tilastawa Gwamnonin bin umarnin nasu, saboda al'umma su san yadda aka salwantar da kudinsu.
Mataimakin Daraktan, ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya baiwa kowanne ɗan ƙasa yancin sanin yadda aka kashe kuɗin da aka warewa Jiharsa.
Ƙungiyar, ta ce cire tallafin man-fetur din da akayi, ba karamin kassara tattalin arzikin da kuma ƙara talauta ƴan ƙasar yayi ba, ta ƙara da cewa kowanne Gwamna da ya gayyato hukumomin nan na yaƙi da Hancin da Rashawa ta EFCC da ICPC wajen bayyana yadda aka kashe kuɗin tallafin.
Komred Kabiru Dakata, Babban Daraktan Cibiyar Wayar da kan Al'umna akan shugabanci nagari da kuma tabbatar da adalci wato KAJA, ya ce wannan mataki da SERAP ta ɗauka abu ne mai kyau, domin yana ɗaya daga cikin hakkin ƴan ƙasa da ƙungiyoyin al'umma da suna bibiyar yadda gwamnatoci suke kashe ƙudin al'umma.
Sannan ba wai kawai ƙungiyar SERAP ce ya kamata ta yi hakan ba, hatta sauran kungiyoyin jihohi ya kamata sun rika bibiyar yadda gwamnoni ke kashe dukiyar jama'a.
A hirarsu da Muryar Amurka, gwamnonin jihohin Jigawa da Yobe ta bakin kakakinsu, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Jigawa Hamisu Gumel, sun tabbatar da cewa sun kashe waɗannan kuɗaɗe ta hanyar da ya dace, kuma talakawa sun ci moriyar tallafin.
Shi ma kakakin Gwamna Jihar Yobe, Mamman Mohammed ya shaida cewa tun kafin tallafin, gwamnatin tarayya ya zo musu, gwamnatin jihar Yobe ta yi nata tallafin, kuma wannan kuɗaɗen da aka ba su sun kashe su ta hanyar da talakawan Jihar suka amfana.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne gwamnonin za su yi mubaya'a game da umarnin Ƙungiyar SERAP, ko kuma za su yi biris da shi?
Ƴan Magana dai na cewa, "ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi".
Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna