Masu Gasa Burodi Sun Yi Bore

Buredi.

Kungiyar masu yin Burodi a Najeriya shiyyar arewa maso gabas ta gudanar da taronta na wannan shekara a garin Gombe, inda ta bada sanar cewar bata amince da sabon tsarin da aka bukace ta, kan ta ringa sa kudaden da take biya sabili da wasu ayyuka da ake gudanar mata, zuwa wani asusun kamfani mai zaman kansa, a maimakon asusun hukumar NAFDAC.

Muhammad Gidado Sani, shine shugaban kungiyar masu gasa burodi na shiyyar arewa maso gabas.

“Mu dai abunda muka sani a baya, da duk wani abunda ya shafi magana na kudi, mukan biya NAFDAC ne ta ‘account’ dinta. Abunda ya faru yanzu, sun hada mu da wasu ‘consultants’ wadda wannan zasu nemi kudi a gunmu kai tsaye. Ba’a asusun NAFDAC zamu sa ba. Wannan wani abu ne sabo, wanda bama goyon baya”.

Adamu Baba Jahun, shine shugaban kungiyar masu gidajen Burodi a Bauci, cewa yayi “shekara aru-aru, tun lokacin da aka kirkiro hukumar NAFDAC, mu muna masu bada goyon baya akan hukumar NAFDAC. Amma mu a shiyyar arewa muna da matsala guda. Shiyyar arewa sanin kowa ne cewa tayi fama da tashe-tashen hankula. Wannan shiyya tamu, gaskiya muna fama da tauyewar tattalin arziki. Kusan yanzu gidajen burodi a arewa maso gabas sun fi dubu biyu, amma yanzu dubu daya duk sun rurrufe.”

Sai dai a cewar babban jami’in hukumar NAFDAC a Jihar Bauci Mr. Steven Laiko, ya shawarci masu gidajen burodin da su kai koken nasu zuwa Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Gasa Burodi Sun Yi Bore – 3’33”