Masu Garkuwa Da Mutane Sun Addabi Yankunan Abuja

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu masu garkuwa da mutane da aka kama a yankunan Abuja.

Matsalar garkuwa da mutane na kara zama babbar barazana ga mazauna wasu yankunan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Lamarin rashin tsaro sanadiyyar addaba da masu garkuwa da mutane ke yi wa wasu yankunan kananan hukumomin Abuja, ya sa al’umomin yankunan tunanin barin gidajensu domin yin gudun hijira.

Duk da alkawarin da gwamnati ta yi na cewa tana daukar matakan da suka kamata na samar da zaman lafiya, amma masun nazari a al’amuran tsaro na ganin faruwar irin wannan lamari a birnin tarayya abin takaici ne.

Wani da ya nemi sakaya sunansa saboda sha'anin tsaro, ya koka akan matsalar garkuwa da mutane, inda ya ce a baya-bayan nan an yi garkuwa da wasu mutum hudu, bayan an amince da kudin fansarsu amma wadanda suka kai kudin su ma aka rike su.

Hakan ya sa ya kwashe iyalansa daga gidansu, suka koma gidan haya a wani yanki na daban.

Sai dai mai kula da harkokin tsaro a ma’aikatar birnin tarayya mallam Adamu Gwary, ya ce tuni har an fara daukar mataki, domin ministan Abuja Mohammed Musa Bello yana tsaye akan kafafunsa.

Gwary ya ce akwai tsare-tsare da ministan ya yi don inganta tsaro a yankunan birnin, ciki har da hada gwiwar sintiri na jami'an tsaro wanda ya hada da yan sanda da Civil Defense da jami'an farin kaya na SSS har ma da sojoji.

Haka kuma, babban Sifeton yan sanda ya ba da tallafi na musamman wanda ake kira Mobile Police Force a turance a birnin tarayya. Adamu Gwary ya ce ministan yana sane tare da sa ido akan duk wani tallafi da za a ba wadanan jami'an tsaron domin su gudanar da aiyukan su ba tare da wata matsala ba.

Sai dai ga mai fashin baki a al'amuran tsaro Salisu Dantata Mahmud, na ganin faruwar irin wanan a babban birnin tarayya abin takaici ne. Dantata ya ba jami'an tsaro shawarar kara inganta hanyoyin samun bayanan sirri saboda a samu nasarar kawo karshen ‘yan ta’adda.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Addabi Yankunan Abuja - 2'46"