Masu Bincike A Harkokin Tsaro Sun Kirkiro Rigakafin Kutse Ta Yanar Gizo

Masu bincike kan harkokin tsaro a Amurka sun kirkiri rigakafin kutsen da ake ta yanar gizo wanda ya shafi dubban kwamfutoci a kasashen duniya daban-daban.

Cikin wannan makon ne masu kutse suka haddasa gagarumin tsaiko ga gwamnatoci da kamfanoni daban-daban na kasashen Turai, lamarin dai yafi tsamari a kasar Ukraine.

An kirkiri manhajar da zata taimaka wajen dakatar da kai dukkan wani hari kan kwamfutoci domin neman kudaden fansa. Aikin manhajar dai shine dakile yiwuwar kaiwa kwamfutoci hari.

Wannan ci gaba dai zai taimakawa kamfanoni wajen kare su ga fadawa hannun masu kutse irin lamarin da ya faru ga kamfanonin kasar Ukraine.

Rahotanni na cewa an sami katsewar al’amura a babbar tashar samar da wutar lantarki ta Ukraine da bankuna da kuma wasu ma’aikatun gwamnati.

Kutsen ya shafi kamfanoni a kasashen Birtaniya da Rasha da kuma Ukraine.

Daga cikin kamfanonin da wannan abu ya shafa har da kamfanin samar da makamashi na Rosneft da AP Moller Maersk.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Bincike A Harkokin Tsaro Sun Kirkiro Rigakafin Kutse Ta Yanar Gizo