Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatoci Na Amfani Da Manhajar Leken Asiri Wajan Yiwa Mutane Kutse


A cewar kwararru a fannin tsaro da kungiyoyin kare hakkin bil Adama sunce gwamnatoci a wasu kasashen duniya na amfani da manhanjar leken asiri wajen kutse cikin wayoyin mutane, domin karanta bayanansu wanda suka hada da sakonnin email da dai sauransu.

Manhajar da ake kira da suna spyware ana amfani da ita ne yayin da mutane ke dogara wajen ajiye muhimman bayanansu a wayoyin zamani.

Shekaru da suka gabata wasu kamfanoni masu zaman kansu sun sayar da ire-iren wannan manhaja, da ake amfani da ita wajen aikawa mutane da sakon kar ta kwana, da zarar mutun ya bude sakon ko ya danna wani adireshi da aka aika masa, to wayar ta shafu da wata kwatar virus wadda zata taikama wajen yiwa wayar kutse.

Kamfanonin na sayarwa da gwamnatoci wannan manhaja kuma suke gargadin ayi amfani da ita ta hanyar da ya kamata, kamar yakar ta’addanci da kuma wasu manyan laifuka.

Labari na baya-bayan nan kan wannan batu an wallafa shi ne a jaridar New York Times, inda gwamnatin kasar Mexico ta mayar da hankali kan masu gwagwarmaya da ‘yan jarida, wajen aika musu da sakonni domin samun hanyar shiga wayoyinsu.

Sai dai kuma gwamnatin Mexico ta musanta hakan, inda ta dage kan cewa idan babu izini daga kotu basa amfani da ita.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:16 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG