Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Ya Dauki Matakin Dakile Amfani Da Hotunan Jabu


Facebook ya fitar da wata sabuwar hanya da zata taimakawa masu shafuka a dandalin kimanin mutane Miliyan 166 kare hotunan da suka kafe na profile.

Kamfanin zai fara gwada sabuwar hanyar ne a kasar Indiya, inda akafi samun korafe-korafe daga wajen mata kan cewa ana daukar hotunansu ana amfani da su ba tare da izininsu ba.

A cewar babbar jami’ar da ke aiki kan wannna sabuwar hanya, Aarti Somon, tace “mutane na ‘daukar hoton da ba nasu ba suyi amfani da shi a wani sabon shafi na daban a matsayin nasu ne.”

Matsalar yin amfani da hotunan mutane wajen kirkirar shafukan jabu ta zama ruwan dare a kasashe masu yawan gaske.

Ba dandalin Facebook ba ne kadai yake fama da wannan matsala ba, wadda kuma ta keta tsarin duk kafafen sada zamunta. Amma babu wata kafa da ta fara daukar matakin dakile faruwar hakan sai Facebook.

A cewar Farfesa Mary Anne Franks ta jami’ar Miami, daukar matakin da zai hana mutane ‘daukar hotan da ba nasu ba don yin amfani da shi a matsayin na su abu ne da ya kamata. Ana kyautata zaton Facebook zai yi amfani da fasahar gane hoto domin ganin an samu nasara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG