Zaben dai na daukar hankali a kasashen duniya ne duba da cewa ‘yan takarar biyu suna da ilimin sanin makamar mulki, duk da cewa Shugaba Donald Trump dan kasuwa ne shi kuma tsohon mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden masanin ayyukan gwamnati ne.
A wata tattunawa da wani tsohon mazaunin kasar Amurka, Tijjani Adamu sarkin kasuwar Bauchi, ya ce ya ga gwamnatocin Amurka 6 tun daga zamanin Jimmy Carter har zuwa Barack Obama.
Adamu ya ce baban abinda ya sha bamban a yakin neman zaben Amurka da na Najeriya shine kosawar harkokin siyasa. Ma’ana a Amurka, kana iya zaben dan takarar da ba jam’iyyarku daya ba saboda manufofi da kudurorin da ya gabatar, amma ba haka lamarin ya ke ba a wasu kasashen.
Wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Dakta Abdullahi Yelwa, malami a kwlejin fasaha da kere-kere a Bauchi, ya ce zaben Amurka ya na da muhimmanci a fadin duniya saboda ko tattalin arzikin kasashen duniya da dalar Amurka ake auna shi. Bayan haka, a bangaren siyasa da tsaro na kasashen duniya Amurka tamkar kanwa uwar gami ce.
A zaben Amurka na shekarar 2016, an zargi Rasha da yin kutse a harkokin zaben, wani lamari da Dakta Abdullahi ya ce ba abin mamaki ba ne idan Rasha ta yi kokarin yin hakan a wannan karon amma ba lallai ta kasance kan gaba ba. Ya kuma ce komai na iya faruwa a zaben.
Saurari cikaken rahoton Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5