Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN AMURKA: Wadansu Jihohi Zasu Kada kuri’a Kan Halatta Tabar Wiwi


Zaben Amurka na 2020
Zaben Amurka na 2020

A yau 3 ga watan Nuwamba, masu kada kuri’a a New Jersey, zasu yanke hukunci kan ko a halatta amfani da tabar Wiwi a hukumance.

Karamin gari na Bellmawr dake kudancin New Jersey ya shahara wajen amfani da tabar wiwi a matsayin magani don warkar da cututuka.

An halatta amfani da tabar wiwi a matsayin magani a New Jersey a shekarar Agusta 2012. Gwamnan jihar Phil Murphy yana goyon bayan halatta amfani da tabar wiwi don magani.

Gwamnan ya ce “Jihohi 11 da Washington D.C. sun fara ganin tasirin daukar wannan matakin ta fannin samar da ayyukan yi, farfado da tattalin arziki da sake fasalin yadda ake gabatar da kararraki ko samar da dokar kariya sakamakon bada izini da kuma sa ido kan amfani da tabar wiwi”

Tabar Wiwi
Tabar Wiwi

A hira da Amanda Hoover, wata mai sa ido kan batun halatta amfani da tabar ta bayyana cewa, “… kusan rabin kuri’un jin ra’ayin jama’a tun a watan Maris tsakanin kashi 66 zuwa kashi 70 cikin dari na mutane suna bayyana cewa mai yiwuwa su goyi bayan halatta amfani da tabar wiwi don jinya.

Wasu jihohin uku na Amurka suma zasu kada kuri’a yau kan ko a halatta amfani da tabar, ciki har da jihar Arizona da South Dakota da Montana.

Masu goyon bayan kafa dokar sun ce za a samar wa baitulmalin jihar karin kudin shiga kimanin dalar Amurka miliyan 120 a shekara idan aka goyi bayan yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska, domin amfanin wadanda suka manyanta, kuma aikata manyan aifuka zasu ragu.

Wani yana zaben abinda yake bukata a dakin maganin tabar wiwi (AP Photo)
Wani yana zaben abinda yake bukata a dakin maganin tabar wiwi (AP Photo)

Sai dai masu adawa sun na ja da wannan bisa dalilin cewa, tuki zai kasance da hadari kuma gwajin tuki idan mutun ya sha tabar wiwi zai yi wahala kuma da tsada.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a na nuni da cewa, kaso daya bisa uku na mazauna New Jersey,suna da sha’awar a halatta amfani da tabar wiwi.

tsarin-zaben-shugaban-kasa-a-amurka

yau-ake-gudanar-da-zaben-shugaban-kasar-amurka

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG