Masarautun Bauchi Da Dass Sun Yi Tur Da Farmakin Da Wasu Matasa Suka Kai Wa Ayarinsu Kwanan Nan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi)

Masarautar Bauchi da ta Dass a Najeriya sun bukaci gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Bauchi su kafa wani kwamiti da zai binciko matasan da suka ci mutuncinsu a makon da ya gabata.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu matasa suka yi wa ayarin sarakunan gargajiyar kwantan bauna a lokacin da suke kan hanyar zuwa bikin karramawa da tunawa da shugaban al’umar Sayawa marigayi Baba Peter Gonto a karamar hukumar Bogoro, inda suka yi ta jifar motocin ayarin.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a madadin masarautun Bauchi da Dass, ‘Dan Galadiman Bauchi Savior Ibrahim Saidu Jahun, ya shaida cewa wasu bata gari ne marasa kishin kasa suka ingiza matasan don su aikata wannan cin zarafin akan sarakunan.

Shugaban ci gaban Al’ummar Zaar da kuma ake kira Sayawa, Engineer Isuwa Galla, ya yi tattaki zuwa fadar Bauchi da kuma ta Dass don bai wa sarakunan hakuri game da abinda ya faru, daga bisani ya je sakatariyar ‘yan Jarida domin shaida wa duniya rashin jin dadinsu game da abinda ya faru.

Ana hasashen dai an barnata kayayyaki na miliyoyin naira ciki har da gidaje da kuma wasu muhimman abubuwan.

A halin da ake ciki, hukumar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta ce ta na gudanar da bincike kan lamarin, a cewar kwamishinan 'yan sandan jihar Umar Mamman Sanda.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab:

Your browser doesn’t support HTML5

Masarautun Bauchi Da Dass Sun Bukaci Gwamnatin Najeriya Ta Binciko Matasan Da Suka Tozartasu