Masana a Najeriya sun ja hankalin gwamntin tarayya musamman ganin yadda kasar ta dade tana dogaro kan kudaden shigar da take samu daga man fetur, zuwa wasu hanyoyi domin kara inganta kudaden shigar ta.
Malam Yusha’u Aliyu, masanin tattalin arzki ne kuma ya bayyana cewa masana harkokin haraji sun yi kira da a fadada shi zuwa ga talakawa ba masu arziki kadai ba sa’an nan ya kai ga kowane irin aikace-aikace ake yi a cikin kasa.
Masani ya kara da cewa a da, ana bi gida-gida ne ana amsar haraji kamar yadda turawa suka tsara, haka kuma a harkokin Noma da dabbobi, amma tun daga lokacin da sojoji suka fara juyin muki lamarin ya koma su kadai yake amfana da kudaden da ake samu na gwamnatoci, haka kuma siyasar kasar, itama tazo ta kasu kashi biyu, wasu suka alkawarta soke haraji da jangali bayan an zabe su.
Jihar Legas na kan gaba wajan tara kudaden shiga, alal misali, a shekarar 2016, jihar ta tara zunzurutun kudi har Naira Miliyan dubu dari hudu, da talatin da shida da Miliyan dari uku, kuma kimanin talakwan jihar Miliyan biyar ne ke biyan haraji ga gwamnatin jihar, kuma a wannan shekarar ma an yi rajistar mutane dubu dari hudu da ashirin.
Malam Musa Ibrahim, dake sharhi kan al’amurran yau da kullum ya bayyana cewa mafita kawai ita ce kamata yayi gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan ma’adanai, lamarin da shi kuma Dr Abubakar Ummar Karen a jami’ar Abuja, ya kalla ta fuskar dora nauyin akan masu arzikin kasar.
Domin karin bayani saurari rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5