ABUJA, NIGERIA - Rundunonin sojan kasa, na ruwa, da na sama ne suka fi samun kaso mafi tsoka a kasafin na 2023, inda rundunar sojan kasa zata sami naira biliyan dari shida da talatin da takwas da milyan daya.
Kimanin naira biliyan dari biyar da tamanin a cikin wannan adadi aka ware don biyan albashi sai kuma naira biliyan ashirin da hudu don ayyukan yau da kullum, yayin da manyan ayyuka zasu lakume naira miliyan talatin da biyu.
Ita kuma rundunar mayakan sama wacce ta sami sama da naira miliyan dari, manyan ayyuka ne zasu lashe kimanin naira miliyan hamsin.
Baki daya an sami gibin sama da naira tiriliyan daya a kasafin idan aka kwatanta da na bara, abinda ke tada hankalin masana tsaro irin su Dr. Kabiru Adamu. Masanin yace gibin kudin a fannin tsaro na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke kara afka wa yanayin rashin tabbas inda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar kasar.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5