Ra'ayoyin Wasu ‘Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya lashe zaben shugaban kasa na Nuwamba 2024

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum a Jamhuriyar Nijar sun fara bayyana matsayinsu dangane da zaben Amurka na ranar Talata 5 ga watan Nuwamba bayan da aka ayyana dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump a matsayin wanda ya yi nasara a fafatawarsa da Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat.

Wasu daga cikin 'yan kasar sun ayyana Trump a matsayin wanda ya nuna juriya da jajircewa don ganin ya cimma burin shimfida manufofin siyasarsa a wani lokacin da Amurkawa ke bukatar sauyi.

Wannan galaba ta Donald Trump manuniya ce da a fili ke fayyace muhimmancin masu kada kuri’a a mulkin dimokradiya in ji Abdourahamane Alkassoum mai sharhi akan al’amuran siyasar duniya wanda ke cewa karbe shugabancin kasa daga hannun dimokrat don mayar da shi hannun republican abu ne da ke jaddada wayewar talakawan Amurka a maganar zabe.

Amma babban editan jaridar l’independent Plus Jaharou Maman ya dora alhakin faduwar Kamala Harris a wannan zabe kan wasu kure-kuren da ya ce gwamnatin Joe Biden ta tafka a ciki da wajen kasar yayin da Donald trump dan takara ya sami karbuwa a wajen wasu masu bakin fada a ji.

Yanzu kam hankula sun karkata wajen ganin yadda za ta kaya a wa’adi na biyu na mulkin Donald Trump a yayin da al’umomin kasashen duniya ke fatan ganin kasar Amurka ta taka burki wa kashe-kashen da ake zargin gwamnatin Democrat da rufe ido kansu wato yakin Isra’ila da Faledinu da wanda Rasha ta shafe shekaru tana gwabzawa da Ukraine kamar yadda a wani bangaren nasarar ta ‘dan takarar Republican ka iya ta da hankulan bakin haure a Amurka.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayoyin Wasu ‘Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka. MP3