A yau Talata ne ake sa ran mai kamfanin sada zumuncin Facebook, Mark Zuckerberg, zai bayyana gaban wasu ‘yan majalisar dattawan Amurka bayan da ya bada hakuri akan yadda kamfaninsa yayi amfani da bayanan miliyoyin mutane ma’abota shafin.
Shugaban kwamitin shari’a Chuck Grassley ya ce yakamata masu amfani da shafin su san ta yadda aka sami bayannansu da kuma yadda aka yi amfani da su,” ya kuma ce ya na so ya ji daga Zuckerberg yadda kamfanin zai bambance tsakanin kare bayanan jama’a da kuma samun change-change a fannin.
Zuckerberg ya gana da ‘yan majalisar dokoki a sirrance jiya litinin a birnin Washington, ya kuma fidda wani rubutaccen bayani, ya na cewa kamata yayi kamfanin sadarwar yayi iya kokarinsa wajen kare kansa da kuma bayanan masu amfani da shafin FB, ta yadda ba za a iya yin amfani da bayanan ba bisa ka’ida ba.
A bayaninsa, Zuckerberg ya ce kamfanin FB ya fara sanar da mutane miliyan 87 da kamfanin sarrafa bayanan Cambridge Analytica ya yi amfani da bayanan su ba tare da saninsu ba.