Masu sa ido na kungiyar hadin kan Larabawa suna shirin bada rahoto kan halin da ake ciki a kasar Siriya bayan sun shafe wata guda suna sa ido kan yunkurin gwamnati na aiwatar da shirin da zai kawo karshen murkushewa masu zanga zangar da take yi da ake zubar da jini, a tarzomar da aka shafe watanni goma ana gudanarwa.
Wa’adin aikin masu sa ido ya cika yau alhamis, yayinda ministocin harkokin kasashen ketare na kungiyar hadin kan larabawan zasu gana ranar Lahadi domin nazarin rahoton masu sa idon kafin su san mataki na gaba da zasu dauka.
Wani mai sa ido na kungiya ya shaidawa Muryar Amurka cewa, yana kyautata zaton za a kara wa’adin aikin tawagar domin janyesu zai samar da wani gibin da ba za a so ba. Bisa ga cewarshi, ko ba komi kasancewarsu a wurin, ya sa kowa ya maida bakanshi.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Siriya sun kushewa tasirin aikin masu sa idon. Bisa ga cewarsu, shugaba Bashar al-Assad ya rudi masu sa idon ya kuma kara kaimin kai hare hare da ake asarar rayuka tunda masu sa idon suka isa kasar ranar 26 ga watan Disamba.
Sarkin Qatar ya yi kira da a tura dakarun kasashen larabawa Siriya domin hana Mr. Assad ci gaba da murkushe masu zanga zangan dake neman ganin bayan mulkinshi na shekaru 11. Kasar Siriya dai taki amincewa da daukar wannan matakin