Majalisar ta umarci manyan jami'an tsaron ne da su shirya bayyana a zaurenta domin su bada bayanan kokarin ceto 'yan matan Chibok da yanzu suka cika shekaru biyu a hannun 'yan ta'adan Boko Haram.
Sanata Ibrahim Gobir dan majalisar yana ganin duk kokarin da aka yi ba'a yi nasara ba. Hanyar da za'a bi a ci nasara ita ce ta komawa kan binciken kwakwaf tare da taimakon kasashen waje irin su America, China da makamantansu. Idan ba'a nemi taimakonsu ba watakila ba za'a taba ganosu ba. Dalili ke nan da majalisar ta gayyaci manyan jami'an tsaro su ba majalisar shawara. Majalisar kuma zata so ta san inda aka kwana dangane da neman 'yan matan.
Amma majalisar wakilai nada kwarin gwuiwa za'a gano 'yan matan musamman bisa ga wani faifan bidiyo da CNN ya nuna inda aka fitar da hotunan 'yan mata su goma sha biyar da ake kyautata zaton suna cikin 'yan matan dari biyu da goma sha tara.
Haliru Dauda Jika dan majalisar wakilai yace gwamnati ta samu mafita akan lamarin abun da ya kamata a yi shi ne a cigaba da addu'a tare da karawa gwamnati karfin gwuiwan cigaba da yin anfanin kafar da aka samu na dawo da yaran.
Shi ma Garba Cede na majalisar wakilan ya ba gwamnati shawara akan iyayen 'yan matan. Yace a dinga ba iyayen tallafi na musamman maimakon kulawa da 'yan gudun hijira kawai. Kamata ya yi a bisu har gida ana taimaka masu tare da yi masu bayanai masu dadi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5