Manyan Jami’an Nijer Za Su Fara Bayyana Wa Hukumomi Dukiyarsu a Duk Shekara

Majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta kada kuri’ar amincewa da kudirin dokar da gwamnatin kasar ta gabatar don tilastawa manyan jami’an gwamnati bayyana adadin dukiyar da suka mallaka a kowace shekara, a matsayin wani mataki na magance dabi’ar sace-sacen dukiyar kasa da ke kokarin samun gindin zama a ‘yan shekarun nan.

Lura da yadda dabi’ar rub-da-ciki akan dukiyar kasa ke kara tsananta a wajen jami’an gwamnati manya da kanana ya sa gwamnatin ta Nijer ta kudiri aniyar magance wannan matsala da ke barazana ga ci gaban kasa, mafari kenan ta shigar da wani kudirin doka a gaban majalisar dokokin kasar, da nufin samun izinin soma tilastawa manyan ma’aikata su yi wa hukumomi bayanin dukiyar da suka mallaka a karshen kowace shekara, kamar yadda dan majalisar dokokin kasar Boukari Zilly ya bayyana.

Da kuri’u 110 daga cikin 171 ne majalisar ta amince da wannan kudiri, wanda za a zartar da shi a matsayin doka.

A can baya tsarin fayyace dukiyar jami’an hukuma ya tsaya ne kan shugaban kasa, Firai Minista, ministoci, shugaban majallisa da shugabanin hukumomin Jamhuriyya.

A sabon tsarin da gwamnatin ta zo da shi ya hada da ‘yan majalisar dokoki a wannan karon, sai dai a wannan zaman sun cire kansu daga sahun wadanda abin zai shafa.

Dan majalisa Sanoussi Mareni, ya shaida wa Muryar Amurka dalilan daukar wannan mataki, inda ya ce su ‘yan majalisa sai wata ya yi idan sun yi zama ake basu kudin alawus, saboda haka suka ga bai dace a sanya su ciki ba.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Manyan Jami’an Nijer Za Su Fara Bayyana Wa Hukumomi Dukiyarsu a Duk Shekara