Ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shukry ya ce kasarsa tana son kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya hana Habasha daukar wani muhimmin mataki na shirin gina madatsar ruwa daga Kogin Nilu.
Shirin na Habasha na kokari ne ya samarwa kasar wutar lantarki daga kogin ba tare da wata tsayayyar yarjejeniya ba.
Kasar ta Habasha ta ce za ta fara cike gurbin tafkin da ake kira “Grand Renaissance Dam” a watan Yuli bayan da tattaunawar da suke yi da Masar da Sudan ta cije a wani mataki.
A wata tattanawa da kamfanin dillancin labarai na Associated Press, Shukry ya ce akwai nauyi da ya rataya a wuyan Majalisar Dinkin Duniya na maganace duk wata matsala da ke barazana ga zaman lafiya a tsakanin kasa da kasa, yana mai cewa “matakin da Habasha ke shirin dauka na gashin-kanta zai iya haifar da wannan barazana.”
Masar dai ta dogara ne da Kogin na Nilu wajen samar da kashi 90 ciki 100 na ruwan da take amfani da shi, kuma tana tsoron matakin da Habashan ke son dauka zai yi mummunan tasiri idan ba a kula da bukatunta ba.
Ita ma Sudan wacce ta dogara matuka da Kogin na Nilu wajen samun ruwan da take amfani da shi, ta tsinci kanta a tsakanin wannan takaddama da ka iya jefa ta cikin mawuyacin hali.
Facebook Forum