Manoman Nijar Na Neman a Biya Su Kudaden Gonakinsu

Shuwagabannin Najeriya da Chadi, Nijar dakuma Kamaru Zasu Yaki Boko Haram, Oktoba 9, 2014.

Wasu mazauna karkara a yankin Damagaram dake Jamhuriyar Nijar da aka karbi gonakinsu aka gina matatar mai ta Soraz shekaru biyu da suka gabata, na neman a biya su sauran kudadensu da ba a cika musu ba.

An karbi filayen ne a hanun manoman karkara a lokacin da aka gina matatar man a matsayin cewa za a biya su kudaden wadanda aka ba su wani kaso daga ciki.

“Ba mu da wata sana’a illa iyaka noma da kiwo kuma wurin noma da kiwon an zo an kafa masana’anta, ya kamata aduba a gani yadda matsatsi ya nuna, babu hatsi bana.” In ji wani manomi wanda ya bayyana sunansa a matsayin Dan Malam.

A cewar shi ya kamata a yi da wajewa tun da farko kan kudaden da aka basu da kuma abinda ya rage za a cika musu.

Manoman sun kara da cewa ba a yi wa gonakinsu kudi ba, kawai an yanka ne aka fara basu wani kaso.

Sun kuma yi korafin cewa sun daina jin duriyar lauyan dake shiga tsakaninsu da gwamnatin.

Sai dai yunkurin jin ta bakin gwamnatin kan wannan korafi na manoman ya cutura.

Saurari wannan rahoton na wakiliyarmu Tamar Abari domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Manoman Nijar Na Neman a Biya Su Kudaden Gonakinsu - 3'14"