Burin hukumar kiwon lafiya ta duniya ne a samu isasshen jini a kowane asibiti kafin nan da shekarar 2020 domin bukatun masu neman ceto.
Jami'in ayyukan wayar da kawunan al'umma a asibitin karbar jini na kasar Jamhuriyar Nijar Samusa Li cewa yayi har yanzu jama'a basu fahimci fa'idar ba da jini ba a Jamhuriyar Nijar.
Yana mai cewa da kyar suke samun rabin jini da suke bukata bisa ka'idar da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta bayar. Idan kashi daya cikin al'ummar kasa na taimakawa da bada jini ba za'a samu karancinsa ba.
Alhaji Adamu Musa jigon wata kungiya dake fadakar da jama'a akan mahimmancin bada jini yace tunanen abubuwan da ka biyo bayan ba da jini ya sa mutane ke dari dari da ba da jini.Yace mutaun sai shekarunsa sun kai akalla 18 kuma yana da nauyin kilo 50 tare da koshin lafiya kafin ya ba da jini. Amma wasu suna tsoron kada a gano suna da wata cuta idan sun je ba da jini sh ya sa basa zuwa su taimaka. Yace suna yawon fadakar da kawunan mutane.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum