Ma’aunin mizanin ruwan saman yayi nunin cewa, milimita dari da hamsin da shida na ruwan sama ne ya sauka a birnin Nyamai stakanin magaribar talata zuwa safiyar laraba. Lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa da rugujewar gidaje da dama,
Rahotannin wucin gadi na cewa, mutane tara ne suka rasa rayukansu, sai kuma rugujewar gidaje da dama da ake kokarin tantance adadinsu. Ruwan ya kuma yi awon gaba da dukan shagunan kasuwar Gemage dake daya daga cikin fitattun kasuwannin kayan danye dana gwari bisa ga cewar hukumomin birnin Nyame.
Magajin garin Nyame ta uku, Mallam Tini Arzuma ya bayyana cewa, cikin mutanen tara da suka rasu, akwai kananan yara uku.
Dama mazaunan Nyame sun sha korafi a game da karancin magudanan ruwa da rashin matakan kariya irin na zamani, duk kuwa da cewa, suna biyan haraji daidai gwargwado, to amma hukumomin sun dora alhakin wannan matsala a kan talakawan da suke kin mutunta tsarin gine gine da fasalta gari.
Magajin yayi kira ga al’umma da a kula da yadda ake gini. Bisa ga cewarshi, mutane suna zubar da shara a magudanun ruwa abinda ke toshe hanyar ruwa ya haifar da ambaliya.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Sule Mummuni Barma ya aiko daga birnin Nyame.
Facebook Forum