Yayin da aka kusa kammala jigilar maniyatan jihar Taraba daga filin saukar jirgin sama dake Yola su kuwa na jihar Adamawa a bangare guda kuma ko sawu daya ba'a fara yi ba na maniyatan jihar.
Maniyatan jihar Adamawa suna dorawa kamfanin Kabo laifin tsaikon da zargin ya jawo masu. Inji su wai tun da maigidansu ya rasu aka dinga samun jinkiri daga kamfanin. Mai magana da yawun maniyatan yace ya kamata su gyara halinsu idan har suna son nan gaba a sake nemansu. Kamfanin Kabon na jawowa mutane jinkiri da dama.
Wai ko ummara za'a je indan an kawo kamfanin Mass Air mutane suna murna amma idan an ce kamfanin Kabo ne sai murna ta koma ciki, sai hankula kuma su tashi saboda sun san abun da zai faru.
Wadanda suka riga suka baro kananan hukumominsu da sunan za'a tashi yau ko gobe suna nan kara zube sun soma tagayyara. Yawanci basu da wurin kwana sai cikin masallaci ko sansanin alhazai. Da a ce an kawo jirgi an soma jigilar mutane da wurare basu yiwa mutane karanci ba. Ana ganin kamfanin Kabo kamar shekaru sun kamashi.
Kodayake jami'an kamfanin Kambon basu ce komi ba amma da jami'an hukumar alhazai ta jihar Adamawa suka yi tuntuba sai wani jami'in kamfanin yace suna kokarin samun jirgin da zai soma jigilar alhazan.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5