A yayin da sabon suefto janar na 'yan sanda ke kara jaddada ci gaba da aiki da umurnin da ya haramta kafa shingayen 'yan sanda kan hanyoyi a fadin Najeriya, har yanzu wasu bata-garin su na cin karensu babu babbaka.
A Abuja, inda aka dauki kwararan matakan tsaro, mai aikin kamo barayin nan da ya shahara, Ali Kwara, yace ba wai kawai da bata-gari suke yin artabu ba, a wasu lokutan har ma da jami'an tsaro a saboda yaransa su na rike bindigogi, kuma wasunsu su na sanye ne da fararen kaya, abinda ke sanyawa a wasu lokutan suke fuskantar kalubale.
Koda yake ba wai yana dora laifi a kan 'yan sanda ba ne, Ali Kwara yace mutane fararen hula da dama idan sun ga yaransa da bindigogi su kan tuntubi 'yan sanda ko jami'an tsaro wadanda da farko suke daukarsu a zaman 'yan fashi ko kuma 'yan Boko Haram.
Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>
Yace dalilin haka ne yasa suka rage yawan sintiri a Abuja, babban birnin Najeriya duk da cewa ana hada su da 'yan sanda in zasu fita wasu lokutan.
Game da batun yaniin Zamfara, inda barayi da 'yan fashi suka yi tarin yawa a yanzun nan, Ali Kwara yace su na bakin kokarinsu domin kawo karshen wannan lamarin, amma kuma akwai dalilai da dama da suka sanya yawancin irin wadannan bata-gari suka koma ta wancan wurin.
Wasu daga cikin barayin da Ali Kwara ya kama ma sun yi bayanin yadda aka kama su kamar yadda zau ki ji daga bakinsu a cikin wannan rahoto da kuma cikakken bayanin da shi kansa Ali Kwara yayi.