Manhajar Windows 10 Na Ci Gaba Da Samun Karbuwa A Duniya

A yayin wani taron koli da akayi cikin wannan makon kamfanin Microsoft ya bayyana cewa yanzu haka a kwai Kwamfuta har Miliyan 270 da ke amfani da sabuwar manhajar window 10.

Ita dai wannan sabuwar manhaja ta window 10, an fitar da ita cikin shekarar da ta gabata biyo bayan gwaje gwaje da aka shafe lokuta masu tsawo anayi. Tun da aka gabatar da ita ga jama’a, Microsoft na sabunta wannan manhaja akai akai wanda hakan ke nunin lallai har yanzu ana ci gaba da bunkasa manhajar.

Duk da yake dai akwai Miliyoyin kwamfutocin da har yanzu suna amfani da tsohuwar manhajarsu amma Microsoft na ci gaba da aiki tukuru wajen bunkasa kayayyakin kamfanin, kasancewar sabuwar manhajar ba wani dadewa tayi ba, ana ganin cewa tabbas karbuwarta ta wuce ta tsohuwar manhajar window 8 a lokacin da ta fito, Microsoft dai yace window 10 itace manhajar da tafi karbuwa cikin sauri a tarihin kamfanin.

Microsoft ya kara da cewa mutanen dake amfani da window 10 sun shafe sama da awoyi Biliyan 75 suna amfani da ita, akwai sababbin kayayyakin fasaha daban daban har 500 da kamfanin ya kerasu na musamman.