Yayin da ake ta korafe korafe akan fama da matsalar rashin aikin yi a Najeriya, wasu matasa a jahar Adamawa, Arewa maso Gabashin Najeriya sun yunkuro, inda suka rungumi sana'ar ‘Kira domin magance zaman kashe wando da kuma dogaro da kai, kuma tuni kwalliya ta fara biyan kudin Sabulu.
Hakan na zuwa ne alokacin da hankula suka fara kwantawa biyo bayan nasarar da dakarun Najeriya ke ci gaba da samu kan kungiyar Boko Haram.
Mallam Abubakar Aliyu sarkin Lauje da Usman Yahaya Adamu na daga cikin shugabannin wannan masana’anta, kuma sun bayyana yadda wannan sana’a ke tafiya a yanzu. Ita dai wannan Makera ana kiranta ne Makerar Sarkin Lauje, inda manya da matasa harma da yara ke aiki, haka kuma akwai bangarori da dama cikinta inda ake kere keren kayan amfanin yau da kullum musammam ma kayan noma.
A cewar matasan dake aiki wannan Makera, sunce suna koyon sana’a ne domin samun hanyar dogaro da akai, har ma sun nemi tallafin kayan aiki irin na zamani.
An dai dade ana kira ga matasa domin su rungumi sana’ar hannu domin samun hanyar rage zaman kashe wando da mafi yawan matasan Najeriya suka sami kansu a ciki.