Mr. Andy Barnard, da matar shi Sammi, suna da ‘yaya biyu maza, Allah ya basu karuwar ‘ya mace. Tun bayan haihuwar wannan yarinyar babanta Andy, ya ciburi akan yarinyar. Wanda yake fatar Allah, ya nuna mishi ranar auren ta, amma lafiya tazama babban kalubale ga yarinyar Poppy-Mai, tun bayan haihuwar ta har zuwa yau tana da watannin 16.
A lokacin da likitoci suka duba yarinyar an sameta da wata cuta mai tsuro a kwakwalwar mutun, haka daga bisani an sake bincikar ta aka samu tana dauke da cutar kansa a huhu. A dai-dai lokacin da jikinta yayi zafi an kwantar da ita a asibiti na tsawon kwanaki 10, sai daga baya likitoci suka gayama iyayen ta cewar wannan yarinyar bazata rayu ba, suna hasashen bazata wuce kwanaki 2 ba zata mutu.
Hakan dai yasa baban ta Andy, ya dauki yarinyar zuwa gida daga isan su gida ya saka mata kaya irin na amarya a dai-dai lokacin aurenta, wanda ya bayyanar da hakan a matsayin burin shin a rayuwa, yaga ranar da za’ace yarinyar tayi aure. Amma tunda yadda likitoci sukace bazata wuce kwanki 2 ba ta mutu, to bari ya saka mata kaya kamar amarya tayi duk abun da amare keyi a ranar auren su ko ya samu sauki a ranshi na ganin cewar burin shi ya cika.
Bayan sakamata kayan, tayi tafiya da yayunta wanda suka rakata a matsayin dangin amarya a yayin auren ta. Hakan dai yasa uban ta cikin farinciki, duk dai da cewar suna cike da damuwa na rashin lafiyar ta da, kuma makomarta idan har ta mutu.