Manhajar Whatsapp Zata Fara Maida Hankali Akan Shekarun Matasa

Kamfanin Facebook, sashen whatsapp dake da manhajar aika sakon gaggawa, ya kara yawan shekarun matasa masu sha’awar amfani da manhajar whatsapp, daga shekaru goma sha ukku zuwa goma sha shidda, wannan tsarin zai fara aiki a yankin kasashen Turai.

Sabon tsarin da za’a fara wata mai zuwa, anyi shine don bin ka’idojin kare bayanan jama’a.

Ita dai manhajar Whatsapp, zata dinga tanbayar mutane a dai-dai lokacin da suke kokarin saukar da manhajar a wayoyin su, don tantance ko sun kai adadin shekarun da aka kayyade.

Idan sun amince da sabuwar yarjejeniyar, wadda aka yita don kare bayanan jama’a da kamfanin whatsapp ke kokarin yi, musamman a kasar Ireland da za’a saka cikin ‘yan kwanakin nan.

Amma dai duk da haka manhajar ba zata tsananta ba wajen tantace shekarun mutanen. sai dai zata yi tambaya ko mutun ya kai shekaru sha shidda.