Hakan na nufin daukacin kudaden shigar da kungiyar ta United ta samu ya karu da kashi 11 cikin 100 idan aka kwatanta da waccar shekarar da ta gabata.
Washington D.C. —
Kungiyar Manchester United ta kasar Ingila, ta sanar samun fam miliyan 648.4 a shekarar da ta gabata.
Wannan dai tarihi ne da kungiyar ta kafa a gasar Premier League.
Alkaluman baya-bayan da kungiyar ta United ta fitar na zuwa yayin da rahotanni ke cewa hamshakin mai kudin nan dan Birtaniya Jim Ratcliffe na shirin sayen kashi 25 cikin 100 na kungiyar daga masu mallakinta wadanda Amurkawa ne.
Daukacin kudaden shigar da kungiyar ta United ta samu ya karu da kashi 11 cikin 100 idan aka kwatanta da waccar shekarar da ta gabata.
Hakan na faruwa ne duk da cewa kungiyar ta kara ne a gasar Europa kadai ba ta zakarun nahiyar turai da ta fi kayatarwa.