Erik Ten Hag yana da yakinin cewa, Cristiano Ronaldo zai zura karin kwallaye bayan da ya jefa kwallo a lokacin da ya koma cikin jerin ‘yan wasan Manchester United bayan ajiye shi.
Erik Ten Hag, wanda ya yi bayanin ne kan shirin sauya Antony da wuri a wasan da suka doke Sheriff da ci 3-0 a gasar Europa League.
An ajiye Ronaldo ne a wasan da suka tashi canjaras da Chelsea sakamakon kin amincewa ya fito a matsayin wanda zai tsaya a gefe ya jira sai an fidda wani a wasan da suka buga da Tottenham a baya, amma sun yi nasara da ci 3-0, wanda ya tabbatarwa da Red Devils gurbi na biyu a rukunin E.
Wannan ita ce kwallon farko da fitaccen dan wasan kasar Portugal din ya ci a wannan kaka a Old Trafford da Ten Hag, wanda ya ga Diego Dalot da Marcus Rashford suma sun zura kwallo, ya ke da tabbacin cewa, akwai zai sake yin haka nan gaba.
“Ganin Ronaldo ya ci kwallonsa abu ne mai kyau,” in ji Ten Hag yayin hirarsa da BT Sport bayan wasan. “Ya taimaka, kungiyar ta taimaka masa, kuma mun san yana iya karasawa. Yana bukatar kwallo kuma a yanzu ina da yakinin cewa za’a samu karin kwallaye.
“Kwallon da kungiyar ta buga ya yi kyau. Tabbas, kuna fatan ku zura kwallo a zagayen farko, don haka ya dauki dan lokaci kadan, amma mun cancanci zura wannan kwallo.
“A zagaye na biyu, mun zura kwallaye biyu daga buda wasan kuma na gamsu da nasarar saboda ba mu nuna gajiyawa ba. Mun maida hankali kan nasara.”
Babban kocin United kuma ya kare matakin da ya dauka na sauya Antony a hutun rabin lokaci. Sakamakon rashin zura kwallo daga kowanne bangare, dan wasan na Brazil ya fuskanci caccaka na neman nuna bajinta yayin da ya kewaya kwallo a kafarsa sau biyu kafin ya buga da ta fita.
Lokacin da aka tambaye shi ko an sauya tsohon dan wasan kungiyar Ajax saboda abin da ya faru, Ten Hag ya amsa, a’a.