WASHINGTON, D. C. - A cewar wata sanarwa da Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NFIU) ta fitar, Mamu “ya shiga harkar tallafawa ayyukan ta’addanci ta hanyar karba da ba ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane dalar Amurka 200, 000a matsayin kudin fansar wadanda aka yi awon gaba da su a hatsarin jirgin kasa na hanyar Abuja zuwa Kaduna."
Amma a wata wasiƙar da lauyansa J.J. Usman (SAN), wadda ya rattabawa hannu a ranar 25 ga Maris, 2024, kuma ya mika wa shugaban NFIU kwafi, Mamu ya bukaci Antoni Janar din ya janye takardar da ya wallafa mai dauke da jerin sunayen mutanen da ake zargi da daukan nauyin ta’addanci nan da kwanaki bakwai ko kuma ya bayyan a gaban kuliya.
Ya ce ayyana sunansa da ma’aikatar shari’a ta yi ta a matsayin mai daukar nauyin ta’addanci ya musguna masa kuma ba ta yi masa adalci ba.
A halin yanzu dai Mamu yana fuskantar shari’a bisa zargin taimakawa ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022.
Mamu, ya kasance a shekarar 2022, inda aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 10 da suka shafi ta’addanci bayan an kama shi a birnin Alkahira na kasar Masar inda ya nufi Saudiyya.
Sai dai ya musanta aikata laifin da aka karanta masa.