Malaman Addini a Jamhuriyar Naiger Sun Nuna Damuwa da Kalamun 'Yan Siyasar Kasar

.Morou Amadou, ministan shar'a na Jamhuriyar Niger

Kalamun batanci dake fitowa daga bakunan 'yan siyasar kasar jamhuriyar Niger sun sa shugabannin addini sun jawo hankalin 'yan siyasan da yi masu kashedii
A cikin tarihin Jamhuriyar Niger 'yan siyasa basu taba yin anfani da kalamun batanci ba kamar yadda suke yi yanzu, lamarin da ya sa shugabannin addini jan kunnuwansu.

'Yan siyasan Niger sun ta furta kalamun batanci da ka iya gurgunta zamantakewar al'ummar kasar. Manyan malaman da suke shirya wani taro a birnin Niamey sun ce 'yan siyasan na furta kalamun batanci ne da nufin cimma burinsu na siyasa ba tare da yin la'akari da hadin kan kasar ba. Shugabannin sun kira 'yan siyasa da su yi taka tsantsan da irin kalamun dake fitowa daga bakunansu.

Kasar Niger dai ba'a san 'yan siyasanta da yin anfani da kalamun batanci ba. To amma a wani lamarin da ya tsorata shugabannin addinin Musulunci sai gashi an wayi gari 'yan siyasa na zage-zage.Dalili ke nan suka kira taronsu.

Yanzu haka dai guguwar rudani da tayar da hankalin jama'a sai kadawa takeyi a kasar inda kalamun da 'yan siyasa ke anfani dasu ba na ban bancin siyasa ba ne kawai a'a har dama na kabilanci.

Idan an duba baya kasar Niger kila ita ce tafi talauci amma yakamata a jinjina mata da irin halin zaman cudanya tsakanin al'ummarta duk da cewa akasarin 'yan kasar Muslmi ne. Shugaban taron Shekh Mustapha Bashir yace "Yanzu 'yan siyasa wurin neman kujera suna so su kawo mana abun da Niger bata gada ba. Niger ta gaji zaman lafiya".

Sheik yace sun gane cewa abun dake faruwa ya nuna kawunansu suke so ba kasar ba. Yace to suna sanardasu su kuka da kansu game da irin maganganun da suke yi. Bayan haka ya yiwa 'yan jarida kashedi game da irin tambayoyin da suke yiwa 'yansiyasa. Yace tambayoyi ne da zasu sa 'yan siyasa su furta abun da zai tada hankalin mutane. Su ma an ja masu kunne tare da 'yan siyasa masu iko. Yan jarida su kaucewa abun da zai kawo rabuwar kawuna a kasar.

Your browser doesn’t support HTML5

Malaman Addini a Jamhuriyar Niger Sun Nuna Damuwa da Kalamun 'Yan Siyasar Kasar - 2:56