Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jam'iyyar MNSD da Aka Kora Sun yi Babban Taro


Seini Oumarou, Shugaban jam'iyyar MNSD mai adawa a Nijar.
Seini Oumarou, Shugaban jam'iyyar MNSD mai adawa a Nijar.

Orarrun sun gudanar da taronsu a Tillaberi, inda aka ce shugaban jam'iyyar Seini Oumarou, ya fi karfi da tasiri.

Jami'an jam'iyyar adawa ta MNSD-Nasara a Jamhuriyar Nijar wadanda aka kora daga wannan jam'iyya a makon da ya shige, sun gudanar da wani babban taron magoya bayansu domin su nunawa sauran 'ya'yan jam'iyyar da ma al'ummar Nijar cewa har yanzu su na da tasiri cikin wannan jam'iyya.

A makon jiya ne, wani taro na kwamitin zartaswar jam'iyyar MNSD ya bayarda sanarwar korar manyan jami'ai guda 9 wadanda suka yi watsi da umurnin jam'iyyar suka kuma je suka shiga cikin gwamnatin hadin kan kasa ta shugaba Mahamadou Issoufou.

An gudanar da wannan babban taro na korarrun jam'iyyar ta MNSD a garin Tillaberi, inda aka ce shugaban jam'iyyar MNSD, Seini Oumarou, yana da karfi da tasiri, kuma daga inda wakilin Muryar Amurka, Abdoulaye Mamane Amadou, ya aiko mana da wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG