Abokiyar aiki Halima ta samu ta zanta da Farfasa Bube Namaiwa shehun malami a Jami'ar Chejh Auta Diop dake kasar Senegal inda yayi fashin baki dangane da wadannan batutuwan.
Bisa ga maganganu Farfasa Namaiwa yace "Abun da nake so 'yan Niger su gane shi ne cikin wannan yanayin akwai wasu wajaje inda shi tsohon shugaban kasa yayi magana da harshen damo. Amma abu maimahimmanci shi ne inda ake tsammanin akwai kudin domin magana ta rabu kashi biyu.'Yan adawa suna neman a yi binciken wancan iko na soja na Salihu Djibo domin sun zargeshi da cewa yayi rufdaciki da kudi da ya tarar a fadar shugaban kasa Tandja Manmadou a zamanin da yayi masa juyin mulki. Su kuma wadannan ma'ikanta suna neman kamar su wanke kansu bisa ga irin abun da ya faru in fa abun ya faru. Na daya kenan. Na biyu yanayin siyasa kowa yana neman inda kishiyarta zata yi wani dan kuskure a samu a damketa, wato ana hangen gaba kenan, zabe mai zuwa. Ina ganin wannan magana ta Tandja Manmmadou ta jawo ana neman a je a bincika. Ina nufin 'yan adawa suna neman su shafa kashin kaji su kuma masu iko suna neman su wanke kansu"
Da ya cigaba da bayani yace shi Tandja Manmmadou abun da ya nuna kudin ba'a cikin baitulmali suke ba. Kudin basa inda su 'yan siyasa ke tsammani amma kudin suna cikin wani banki a Jiddah kasar Saudiya, wato banki na masu aiki da addinin Musulunci. Kudaden jari ne suke a cikin bankin. Ban da haka tsohon shugaban ya nuna akwai ajiyar sefa miliyan dari wadda kamar rigakafin yunwa ce. Bayan babatun da mutane suka yi tsohon shugaban ya fito yayi bayani. Farfasa yace "tun cikin waccan maganar bai ce kudin na cikin baitulmali ba. Na saurara da kyau. Yace na bar masu miliyan dari hudu amma bai ce a cikin baitulmali ba.
Dangane da kiraye-kirayen cewa a tsige kakakin majalisar dokoki Farfasa yace "Wannan kuma a siyasance ne yake fitowa. Ai ba yanzu ba ne wannan maganar take amma a yanzu abun da suke zarginshi da shi in yayi shi, ban tabbatar da yayi shi ba tun da ni ban ji yayi wannan magana ba... Ban tabbatar da ko yayi ta ba...Amma dattijo baya irin wadannan maganganun da yake yi...Akwai ababe da yawa da ya zanto ribarmu ce...Akwai wasu daratsi a wasu kasashe ya kamata mu tsaya mu yi koyi da su...Akwi wasu fannoni da bai kamata 'yan siyasar Niger su shiga ba. In ya shiga a kan gaskiya baya da 'yancin yayi hakan"
To saidai Farfasa yayi kashedi cewa kada su tsige Hamma Amadou abun ya kawo wani cecekuce a kasar da ka iya kaiga rashin kwanciyar hankali. Ya gargadesu su yi hakuri da juna domin nan da shekara biyu za'a sake yin zabe.