Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kano ta Je Makarantar Hadin Gwiwa a Nijar


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

A Jamhuriyar Nijer wata tawagar gwamnatin jihar kano a karkashin jagorancin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ta ziyarci makarantar hadin guywar kasar Nijer da jihar Kano wacce gwamnatin Kano ta gina a birnin Niamey.

Burin gwamnatin kasashen biyu shine na kara dankon zumunci tsakanin yaran kasashen biyu tare da ilmantar da yaran kasashen a harshen fransanci da turancin ingilishi

Kimanin dalibai dari biyu da daya ne suke daukar karatu a wannan makarantar wacce gwamnatin Nijar da jihar Kano suka dauki alwashin kafawa tun a shekarun 2012 a lokacin da gwaman ya kai ziyara Janhuriyar Nijar domin kara dankon zumunci tsakanin al-ummomin kasashen biyu.

Tun wannan lokaci, wannan shine karo na farko kennan da gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci wannan makaranta.

Gwamnan yace “abun sha’awa kun gani dai gashi munzo zaga wajen kwana, mun zaga wajen karatu, mun je wajenda yara suke zuwa asibiti, a cikin wannan makaranta, ga massalacin su, ga bandakai, da wajen cin abinci.”

“Kamar yadda kuka gani, abun sha’awa shine wadannan yara, bacin zasu kara dankon zumunci a tsakaninsu, wadannan yara suna magana a harshen faransaci, da kuma turanci”, a cewar Mr. Kwankwaso.

Banda wannan makaranta, gwamnatin jihar Kano na shirin kafa wata makaranta a jihar Damagaram amma ta mata zalla wadanda zasu fito daga kasashen biyu.

Gwamnan jihar Kanon yace “muna tunanin zamu yi wata, wacce take can a kusa da Najeriya, musamman a Damagaram ta mata, wadda za’a kawo mata daga Kano”.

Ita kuma gwamnatin Janhuriyar Nijar, ta bakin ministan ilimin makarantun boko, Hajiya Aishatu Ummani ta tabbatarwa gwamnatin jihar Kano yin kulawa ta musamman, domin girmama mutunci da kimar makarantar ta hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kano da Janhuriyar Nijar.

Hajiya Aishatu tace “bata yiwuwa ne mutum yayi shuka ya barta ta lalace. Kennan, inshama Allahu, yanda anka kawo wanga, anka girka shi, zai yadu. Ba mu ba, har jikokinmu zasu amfana”.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG