NIAMEY, NIGER - To sai dai wasu ‘yan siyasar na ganin muddin ba a kwaskware dokokin da suka shata tsarin tafiyar da jam’iyun siyasa ba zai yi wuya a cimma burin da aka sa gaba.
Ainahi ‘yan hamayya ne suka nuna bukatar ganin an sake duba tsarin tafiyar majalissar sasanta rigingimun siyasa, saboda haka bayan ganawar da aka yi a tsakanin jagoran ‘yan adawa Tahirou Saidou da shugaban majalissar ta CNDP Firai Minister Ouhoumoudou Mahamadou zaman majalissar na ranar 9 ga watan Satumban 2022 ya kafa kwamitin da zai bada shawarwarin da suka dace wanda bayan nazarin watanni a kalla uku ya gabatar da rahotonsa da yammacin jiya Laraba.
Hurumin majalisar ta CNDP na tsarin tafiyar da ayyukanta wadanda suka hada da hanyoyin da suka dace a bi wajen kiran zaman majalisar da yadda ya kamata a yanke shawarar da aka tsayar da matakan yin sulhu na daga cikin mahimman ka’idodin da kwamitin ya yi wa gyarar fuska.
Matakin da Firai Minista Ouhoumoudou shugaban majalisar CNDP ya ce zai bai wa majalisar damar yin ayyukanta na mai riga kafin barkewar rikicin siyasa kuma mai yayyafa ruwa a irin wadanan rigingimu.
Shugaban jam’iyar Moden lumana bugo da kari madugun ‘yan adawa Tahirou Saidou ya yaba da wannan aiki.
Ya ce Sakamakon ayyukan da wannan kwamiti ya gudanar abu ne dake nuna cewa muna kan hanyar samun nasarorin da ke bada damar ci gaba da tattauna dukkan batutuwan da suka shafi daukacin ‘yan kasa.
Sai dai sakataren kwamitin zartaswar jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki, Kalla Hankouaro na ganin bukatar duba dokokin da suka shata tsarin kafa jam’iyun siyasa matsawar a na fatan magance kace nace a fagen siyasar Nijar.
To amma a na sa ra’ayin shugaban jam’iyar MDN Kokari, Annabo Soumaila, ya ce kwaskware dokokin tafiyar da jam’iyun siyasa tamkar yi wa dimokardiya zagon kasa ne.
A shekarar 2004 ne aka kafa majalissar CNDP a nan Nijar a bisa shawarar hukumar UNDP da nufin rigakafin tashin hatsaniyar siyasar da kasar ta fuskanta a farkon shekarun 1990. Sai dai rashin gamsuwa da abinda suka kira rashin adalcin da masu mulki ke nuna masu ya sa ‘yan hamayya kaurace wa zaman majalisar a jajibirin zaben 2016 kafin su amsa tayin sulhun da shugaba Mohamed Baoum ya yi masu a bara.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5